Ronaldo da Salah sun samu lambobin duniya

Mohamed Salah ya taka rawa a kungiyarsa ta Roma sosai

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto,

Mohamed Salah ya taimaka wa Masar ta samu gurbin gasar Kofin Kasashen Afirka, sannan ya taimaka wa Roma sosai

Dan wasan Masar na Roma Mohamed Salah ya samu kyautar gwarzon dan kwallon kafa Balarabe na 2016, yayin da Ronaldo ya samu kyautar gwarzon dan kwallon duniya ta Globe Soccer Awards, a Dubai.

Wannan shi ne karo na hudu da Ronaldo mai shekara 31, wanda yake rike da lambar gwarzon dan kwallon duniya ta Fifa (Ballon D'Or )ta bana, ya ci wannan lamba.

Shugaban Real Madrid Florentino Perez ne ya karbar wa Ronaldo kyautar kasancewar ba ya wurin a ranar Talata da aka yi bikin.

Amma Ronaldon ya bayyana godiyarsa ta hoton bidiyo da aka nuno shi kai tsaye ga mahalatta taron.

Cristiano Ronaldo ya samu kyautar gwarzon dan kwallon ne, ta Globe Soccer Awards, saboda nasarorinsa na kungiya da kasarsa, sannan Fernando Santos ya samu ta gwarzon koci na shekara, saboda jagorantar Portugal ta dauki Kofin Kasashen Turai na 2016.

Shi kuwa Mohamed Salah mai shekara 24, ya samu kyautar sakamakon kwallo18 da ya ci wa Roma a 2016, abin da ya sa suka gama gasar Serie A ta Italiya a matsayi na uku, da kuma kai su zagayen 'yan 16 na kofin Zakarun Turai.

Kwazon Salah bai tsaya a kungiyarsa Roma ba kadai, domin ya taimaka wa kasarsa Masar ta samu gurbin gasar cin Kofin Afirka ta 2017 da za a yi a Gabon.

Ya yi wannan kokari ne bayan kasa zuwa gasar uku a baya, inda ya ci wa kasar tasa kwallo biyar a wasannin neman gurbin gasar ta Kofin Afirka.

Tsohon dan wasan na kungiyar Arab Contractors da Chelsea ya doke irin su Riyad Mahrez da Islam Slimani da dan wasan Moroko Mehdi Benatia, wanda ya ci kyautar a 2014.

Shi kuwa alkalin wasa Mark Clattenburg, na Ingila, wanda zai jagoranci wasan hamayya na Premier Masar na birnin Alkahira tsakanin Al Ahly da Zamalek ranar Alhamis, ya samu kyautar gwarzon alkalin wasa na shekara.