Berbatov na son komawa Premier

Dimitar Berbatov a kungiya PAOK Salonika

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Dimitar Berbatov a lokacin da yake wasa a kungiyar PAOK Salonika ta Girka

Tsohon dan wasan Manchester United Dimitar Berbatov ya zaku ya koma gasar Premier kamar yadda wakilinsa ya bayyana.

Tsohon kyaftin din na Bulgaria mai shekara 35, ba ya wata kungiya tun lokacin da kungiyar PAOK Salonika ta kasar Girka ta sake shi a watan Yuni.

Wakilin Berbatov, Emil Dantchev, ya gaya wa BBC cewa, ''Dimitar yana jin zai iya cigaba da wasa akalla zuwa karin shekara daya, kuma burinsa shi ne ya koma Ingila.

Tsohon kocin Swansea Bob Bradley a baya ya ce Berbatov na daga cikin 'yan wasan da ke ransa.

A da ana rade radin cewa tsohon dan wasan gaban na Tottenham da Fulham, wanda ya yi wasannin Premier 229 a shekara tara, zai tafi gasar lig din Amurka ne.

Yana cikin tawagar 'yan wasan Manchester United da ta dauki kofin Premier a 2009 da 2011, lokacin da shi da Carlos Tevez suka ci kyautar dan wasan da ya fi cin kwallo a shekara.

Berbatov na benci a lokacin wasan karshe na Kofin Zakarun Turai na 2009, wanda Barcelona ta yi nasara a kan Man United.

Dan wasan ya kuma ci kofin kalubale na lig na Ingila, da Man United da kuma Tottenham, inda ya ci wa Spurs kwallo lokacin da suka doke Chelsea 2-1 a 2008.