Christopher Katongo na shirin zama koci

Katongo yana tunanin ci gaba da wasa har ya kai shekara 40

Asalin hoton, chriskatongo

Bayanan hoto,

Katongo na ganin zai iya ci gaba da taka leda har ya kai kusanshekara 40

Tsohon kyaftin din Zambia Christopher Katongo ya fara nazarin zama koci domin yana duba yuwuwar shiga aikin horarwar.

Dan wasan mai shekara 34, wanda ya jagoranci kasarsa ta ci kofin kasashen Afirka na 2012, har yanzu yana yi wa babbar kungiya ta Green Buffaloes a Zambia wasa.

Katongo ya gaya wa BBC cewa: "har yanzu ina tunanin ci gaba da taka leda. Amma bayan na yi ritaya, zan duba abin da zan yi a gaba, kuma aikin koci na daga ciki, saboda haka ne ma na fara samun horo a kai.''