Klopp: Coutinho ba zai yi wasanmu da City ba

Philippe Coutinho lokacin da ya ji rauni

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Philippe Coutinho ya ci kwallo biyar kuma ya bayar an ci shida a Premier bana

Kocin Liverpool Jurgen Klopp, ya tabbatar cewa Philippe Coutinho ba zai dawo wasa ba daga jinyar da yake yi, har ya buga wasansu da Manchester City ranar jajiberin sabuwar shekara.

Gwanin dan wasan na Brazil mai shekara 24, bai yi wasa shida ba saboda ciwon da ya ji a kafa, a wasansu da Sunderland a watan Nuwamba.

Kocin ya ce: "wasan City ya yi kusa sosai, kuma shi kansa wasan Sunderland ma ranar Litinin ya yi kusa sosai."

Haka kuma Klopp ya tabbatar da cewa dan wasansu na baya Joel Matip ba zai yi wasansu da City ba saboda raunin da ya ji a kafa shi ma.

A ranar Asabar ne abokan hamayyar za su fafata a Anfield (17:30 GMT), yayin da Liverpool ta biyu a tebur take gaban City da maki daya.