Wasu abubuwa da suka faru a fagen wasanni a 2016

  • Mohammed Abdu
  • BBC Hausa, Abuja
Fagen wasanni

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wasu manyan batutuwan da suka faru a fagen wasanni a shekarar 2016

Shekara ta 2016 sai san barka ga wasu 'yan wasan da jami'ai da mahukunta, bayan da suka yi bajinta a fage da dama.

Haka kuma shekara ce da ta ci karo da kalubale a fanni da dama, ciki har da batun cin hanci da rashawa da batun shan abubuwa masu kara kuzarin wasanni.

Wasu kuwa jami'ai da 'yan wasa ba su kai ga karshen shekarar ta 2016 da muke ban kwana da ita ba.

Mohammed Abdu Mam'man Skeeper ya yi bitar wasu daga cikin mahimman abubuwa da suka faru a shekara ta 2016.

A cikin watan Janairu ne a wasan tennis Roger Federer ya kai wasan karshe a Brisbane, bayan da ya doke Dominic Thiem da ci 6-1 da kuma 6-4 a wasan daf da karshe, inda Raonic ya fitar da Bernard Tomic da ci 7-6 (7-5) 7-6 (7-5).

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Tsohon zakaran kwallon tennis na duniya Roger Federer

Guardiola ya koma Man City

Ita kuwa Victoria Azarenka ta lashe kofin farko a gasar kwallon tennis wanda rabon da ta yi hakan tun a shekarar 2013, bayan da ta doke Angelique Kerber a karawar da suka yi a Brisbane.

A dai watan ne Guardiola ya sanar da cewar zai yi ritaya daga horas da Bayern Munich a cikin watan Mayu, bayan shekaru uku da ya yi a can, domin komawa Manchester City.

A karshen watan na Janairu Hukumar wasannin motsa-jiki ta duniya ta tabbatar wa tawagogin 'yan wasan da za su halarci gasarta a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil cewa babu abin da zai same su, duk da annobar Zika da ta barke a kasar.

BBC ta gano cewa kamfanin Adidas mai yin kayan sawa na wasanni, yana shirin kawo karshen yarjejeniyarsa ta miliyoyin dala da hukumar shirya wasannin tsalle-tsalle da guje-guje, IAAF saboda badakalar amfani da kwayoyi masu kara kuzari da aka bankado a wasannin.

A ranar 28 ga watan Fabrairu Ebola ya buge Mai takwasara a turmi na biyu yayin damben ajon Anas dan Sarkin fawa da aka yi a birnin Zariayan jihar Kaduna Nigeria .

Bayanan hoto,

Haduwar farko da Ebola ya buge Mai Takwasara a damben da suka yi a Zaria jihar Kaduna Nigeria

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

A kuma makon karshe a cikin Fabrairu ne aka fara gasar Premier Nigeria wasannin farko.

A farkon makon watan Maris na shekarar 2016 Leicester ta ci gaba da jan ragamar teburin Premier.

A ranar 6 ga watan Maris din shekarar 2016 Barcelona ta tsawaita yawan yin wasanni 36 a jere ba tare da an doke ta ba, wadda a ranar ta doke Eibar da ci 4-0 a gasar La Liga da suka fafata.

A gasar cin kofin zakarun Turai kuwa Barcelona ta fitar da Arsenal bayan da ta doke ta da ci 3-1, da hakan ne kuma Barcelona ta yi wasanni 38 a jere ba tare da an doke ta ba.

Sannan Real Madrid ta takawa Barcelona burki kan yawan buga wasanni 39 a jere ba a doke ta ba.

Paris St Germain ta lashe kofi

A kuma cikin watan ne Watford ta fitar da Arsenal daga gasar kofin kalubale na Ingila bayan da ta doke ta da ci 2-1 a Emirates. A lokacin Arsenal ce ke rike da kofin wanda ta yi ban kwana da shi.

A dai cikin watan ne Paris St Germain ta lashe kofin kwallon kafa na gasar Faransa duk da saura watanni biyu a kammala wasannin.

A kuma lokacin ne Enyimba ta Aba ta doke Vitalo ta Burundi da ci 5-1 a gasar cin kofin zakarun nahiyar Afirka.

A karshen watan Maris Super Eagles da Masar suka tashi kunnen doki 1-1 a Kaduna, inda filin wasa na Ahmadu Bello ya yi cikar kwari.

Bayanan hoto,

Yadda filin wasa na Ahmadu Bello da ke garin Kaduna Nigeria ya cika da 'yan kallo

A kuma karshen watan na Maris ne hukumar gudunar da gasar Firimiyar Nigeria ta ci tarar mai kungiyar Ifeanyi Ubah sama da miliyan biyu da rabi, bayan da aka nuna shi a faifan bidiyo ya mari mai tsaron ragar Heatland Ebele Obi.

A nahiyar Afirka kuwa a cikin watan ne kasar Togo ta nada Claude Le Roy a matsayin kociyan da zai ja ragamar tawagar kwallon kafar kasar kan yarjejeniyar shekara uku.

A watan Afirilu ne kungiyar damben gargajiya ta kasa karkashin jagoranci Ali Zuma ta hada wasan dambe na kasa a jihar Sokoto Nigeria.

A lokacin ne aka sake yin karan batta tsakanin Ebola da mai takwasara, inda a ranar Asabar din mako na biyu suka kasa yin wasa duk da 'yan wasan biyu sun daura aniyar dambatawa.

Sai a washe gari ne suka yi turmi uku babu kisa, Ebola na bin Mai takwasara kisan dambe daya.

A dai fagen damben amma na boksin Anthony Joshua ya zama zakaran duniya bayan da ya samu nasarar yi wa Chales Martin bugun kwaf daya a turmi na biyu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Tsohon zakaran damben boksin Anthony Joshua

Hakan kuma ya sa ya zama dan wasan boksin da ya zama zakara a karancin fafatawa 16 da ya yi fiye da Muhammad Ali wanda ya yi 20 da Mike tyson wanda ya yi 28 kafin su zama zakarun duniya a wasan.

A watan na Afrilu ne aka dakatar da Gonzalo Higuain, na Napoli daga buga wasanni hudu, bayan da ya maida martani cikin fushi, kan jan katin da aka ba shi a karawar da Udinese ta doke Napoli da ci 3-1 a gasar Serie A.

A dai watan ne Chelsea ta nada Antonio Conte a matsayin kociyanta domin maye gurbin Guus Hiddink.

Hiddink, wanda ya maye gurbin Jose Mourinho a lokacin aka amince ya ci gaba da jan ragamar kungiyar zuwa karshen kakar wasannin shekarar.

A cikin watan na Afrilu dai hukumar kwallon kafar Nigeria ta sake fadawa rikita-rikita kan takaddama da take yi da Chriss Giwa wanda har hukumar kwallon kafa ta duniya ta ce za ta dakatar da kasar daga shiga sabgogin tamaula.

Amma hakan bai hana gasar La Liga ta kulla yarjejeniyar aiki tare da ta gasar Premier kasar ba.

A farkon watan Mayu na wannan shekara mai karewa ne, Hukumar kwallon kafa ta Afrika ta sauya tsarin gasar cin kofin zakarun Afrika ta Champions League da kuma ta Confederation Cup, da za a yi a 2017.

Yanzu haka dai kungiyoyin wasa 16 ne za su samu gurbin shiga kowacce daga cikin gasar, a inda za a raba su zuwa aji hudu kuma kowane aji zai kunshi kungiyoyi hudu.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Leicester City ce ta lashe kofin Premier a karon farko

A cikin watan na Mayu Leicester City ta yi wani abin almara inda ta lashe kofin Premier a karon farko shekara sama da 132 da kafa ta.

Bayan buga wasanni 38 a gasar, Leicester ta ci guda 23 ta kuma yi canjaras a wasanni 12 aka doke ta sau uku kacal, ta ci kwallaye 68 aka zura mata 36 a raga ta hada maki 81.

A ranar Lahadi 15 ga watan Mayun 2016 aka kammala gasar La Ligar Spaniya, wanda Barcelona ta lashe kofin shekarar kuma na 24 jumulla. Luis Suarez ne ya ci kwallaye 40 a gasar kuma shi ne wanda ya fi yawan zura kwallo a raga a wasannin nahiyar Turai a kakar.

A can Italiya a gasar Serie A, Juventus ce ta lashe kofin kuma na 32 jumulla, yayin da Gonzalo Higuine na Napoli ya dauki kyautar wanda ya fi cin kwallaye a raga, inda ya ci guda 36.

Ita kuwa Bayern Munich ce ta dauki kofin Bundesliga ne a watan na Maya, wanda kuma shi ne na 26 jumulla kuma Roberto Lewandoski na kungiyar ne ya ci kwallaye 30 a gasar.

Bayanan hoto,

Mourinho sabon kociyan Manchester United

A watan ne aka tabbatar da nadin Jose Mourinho a matsayin sabon kocin kungiyar Manchester United bayan ya saka hannu a kontiragin shekara uku.

Mourinho ya maye gurbin Louis Van Gaal, wanda aka sallama kwanaki biyu bayan da kungiyar ta lashe kofin FA.

A kuma cikin watan na Mayu ne kuma aka sa kyautar mota a gasar damben gargajiya a Minna ta jihar Niger ta Nigeria, amma ba a kammala wasannin ba sakamakon takaddama.

A watan ne a ranar Asabar 28 ga shi Real Madrid ta lashe kofin zakarun Turai na 11, bayan da ta ci Atletico Madrid 5-3 a bugun fenariti, bayan tashi kunnen doki 1-1 tun farko.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo

A kuma watan Yuni aka raba jadawalin wasan damben gargajiya domin lashe kyautar motar hawa a gidan damben Ado Bayero Square da ke birnin Kano.

A lokacin aka zabo 'yan wasa guda shida daga bangaren Guramada da guda shida daga Arewa da kuma guda shida da suke kare martabar Kudu.

Daga karshen wasannin Ebola dan damben Kudu ne ya lashe motar da aka saka, bayan da ya doke Bahagon Sanin Kurna a turmin farko a filin wasa na Kano Pillars da ke Sabon Gari.

Bayanan hoto,

Motar da Ebola ya lashe a damben Kano

A watan dai na Yuni hukumar gudanar da gasar Firimiyar Nigeria ta shirya halartar wasan sada zumunta da wasu kungiyoyin da ke buga gasar Laligar Spaniya.

Hukumar ta ce za ta zabi fitattun 'yan wasan gasarta domin karawa da na Spaniya a ranar 10 zuwa 13 ga watan Agusta.

A watan Yuli kuwa Nigeria ta nada Mikel Obi a matsayin kyaftin din tawagar matasan kasar 'yan shekara 23 da za su buga gasar Olympic.

A lokacin ne a gasar tseren motoci ta Formula One Lewis Hamilton matukin motar Marsandi ya kankane gasar Jamus, inda ya bai wa abokin tserensa matukin motar Marsandi Nico Rosberg tazarar maki 19.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Matukin motar Marsandi Lewis Hamilton

'Yar Birtaniya, Johanna Konta, ta doke Venus Williams, ta kuma lashe babbar gasar wasan tennis a karon farko a Stanford.

A watan na Yuli ne Portugal ta lashe kofin nahiyar Turai a karon farko a tarihi, bayan da ta ci mai masaukin baki Faransa daya mai ban haushi.

Bayanan hoto,

Kofin nahiyar Turai na farko da Portugal ta lashe a tarihi

Wani taron gaggawa da kwamitin Hukumar lafiya ya yi, ya bayyana cewa babu hadari sosai game da yaduwar cutar Zika a lokacin gasar wasanni motsa jika na duniya da za a yi a kasar Brazil.

An dai yi ta kirayen-kirayen cewa ya kamata a jinkirta yin gasar, ko kuma a fasa yi ma baki daya daga kasar.

Tun kafin wasannin 'yan wasan Nigeria suka makale a Amurka, wanda daga baya suka isa Brazil kusan a makare, kuma ba isassun kayan wasanni.

Da aka kammala wasannin na Olympic ne Nigeria ta tsira da tagulla, bayan da Niger ta ci lambar yabo ta Azurfa, inda a wasan Taekwondo, Abdoulrazaka Issoufou Alfaga ne ya samo wa kasar nasarar.

A watan ne Manchester United ta sayi Paul Pogba kan kudi fan miliyan 89 kan yarjejeniyar shekara biyar daga Juventus a matsayin wanda aka saya mafi tsada a duniya a fagen kwallon kafa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Dan wasan da aka saya mafi tsada a duniya a 2016

A cikin watan na Yuli ne dai Chile ta lashe kofin Copa America na shekarar, a kuma gasar ce Lionel Messi ya kafa tarihin yawan ciwa Argentina kwallaye 54 fiye da wadanda Gebriel Batistita ya ci wa kasar.

Haka a dai lokacin ne Lionel Messi ya sanar da yin ritaya daga buga wa Argentina tamaula bayan ya zubar da fenareti a wasan da Chile ta buge kasarsa, kana ta lashe Copa America.

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Dan wasan tawagar Argentina Lionel Messi

Ana shiga Agusta kuwa Argentina ta nada Bouza a matsayin sabon kociyan kasarta. A kuma makon farko na watan aka bude gasar wasannin Olympic a Brazil.

Ana kai wa Satumbakungiyoyin gasar Premier suka kashe sama da fam miliyan daya, wajen cinikayyar 'yan wasan kwallon kafa.

Sam Allardyce ya fara jagorantar tawagar kwallon kafa ta Ingila da kafar dama, bayan da ya ci Slovakia 1-0 a wasan neman shiga gasar kofin duniya da suka kara.

Kociyan Manchester City, Pep Guardiola bai sanya sunan dan wasan kulob din ba, Yaya Toure, a cikin jerin sunayen 'yan wasan da za su takawa kulob din leda, a gasar Champions League ta bana.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Yaya Toure dan kwallon tawagar Ivory Coast

A watan Oktoba Real Madrid ta buga wasa na 400 a Gasar cin Kofin Zakarun Turai a karawar da ta ci Legia Warszawa 5-1 a Santiago Bernabéu.

A watan ne Matukin motar Mercedes, Lewis Hamilton ya lashe tseren motoci ta Formula 1 ta Japan Grand Prix.

Haka kuma matukin Mercedes, Nico Rosberg shi ne ya yi na biyu, sai kuma Sebastian Vettel matukin motar Ferrari ya kammala a mataki na uku a gasar.

A watan na Oktoba ne Ali Kanin Bello dan damben Arewa ya buge Ebola daga Kudu a Kano.

A cikin watan na Oktoba Tyson Fury ya doke Wladimir Klitschko ya kuma lashe kambun WBA da na IBF da na WBO.

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Lokacin da Tyson Fury ya doke Klitschko

Fury mai shekaru 26 ya yi wasanni 24 ba a doke shi ba, yayin da rabon da Klitschko ya yi rashin nasara a dambe tun shekaru 11 da suka wuce.

Enugu Rangers ta lashe kofin Firimiyar Nigeria karo na biyar a watan na Oktoba, bayan da ta ci El-Kanemi Warriors 4-0 a wasan mako na 38 da suka yi, wanda rabon da ta ci kofin tun shekara 32.

Bayanan hoto,

Rangers ce ta lashe kofin Firimiyar Nigeria

A cikin Nuwamba ne Nico Rosberg ya lashe tserensa na motocin Formula 1 na farko na duniya, duk da kin bin umarnin tawagar Marsandi da Hamilton ya yi, bayan da ta bukaci direban da ka da ya dauki tseren a matsayin na Hamayya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Rosberg ne ya ci gasare tseren motoci ta shekarar 2016

Andy Murray ya dare mataki na daya a jerin wadan da suke kan gaba a wasan kwallon tennis a duniya, bayan da ya lashe gasar kwararru ta Paris, hakan ya sa ya maye gurbin Novak Djokovich

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A karon farko Murray ya dare mataki na daya a jerin wadanda suka fi iya kwallon tennis a duniya

A watan Disambar da muke ciki ne zakaran tseren motocin Formula 1 na duniya Nico Rosberg ya sanar da cewa ya yi ritaya nan take.

Dan tseren dan kasar Jamus mai shekara 31 ya ci babbar gasarsa ta farko ranar Lahadi, bayan ya doke Lewis Hamilton.

A cikin watan ne dai Real Madrid ta lashe kofin duniya na zakarun nahiyoyi kuma karo na biyu a Japan.

A cikin watan ne Super Falcons ta ci kofin nahiyar Afirka a Kamaru, bayan da ta doke mai masaukin baki daya mai ban haushi.

Asalin hoton, Super Sports

Bayanan hoto,

Super Falcons ta ci kofin nahiyar Turai

Sai dai kuma tawagar ta yi zanga-zangar kan kin biyan hakkokinta, bayan nasarar da ta yi daga baya aka sasanta.

Bayanan bidiyo,

A ranar Juma'a NFF ta ce ta bai wa 'yan Super Falcons kudin da suke bin ta bashi

A dai wannan watan ne kotun daukaka kararrakin wasanni ta duniya ta rage hukuncin hana Real Madrid sayen 'yan wasan tamaula zuwa kakar wasa daya daga biyu da aka yanke mata a baya can.

Shekara ta 2016 ta yi fama da badakalar cin hanci da rashawa musamman a hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa, ga batun shan kwayoyi masu kara kuzari, wanda ya shafi kasar Rasha a gasar Olympic bayan da aka dakatar mata da wasu 'yan wasan.

A kuma gasar ce aka samu jami'an Kenya da yin sama da fadi.....

Pierre-Emerick Aubameyang na Gabon mai taka leda a Borussia Dortmund ba zai manata da 2016 ba, domin a farkon shekarar ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafar Afirka da maki 143.

Haka ma Riyad Mahrez da ya ci kyautar gwarzon gasar Premier da 'yan wasa suka zabe shi sannan ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka da BBC ta karrama.

Bayanan bidiyo,

Riyad Mahrez ya lashe kyautar Gwarzon Kwallon Afirka na BBC na 2016.

Shi ma Cristiano Ronaldo ba zai mance da 2016 ba, domin shi ne ya ci kyautar Ballon d'Or,

Sai dai kuma wasu jami'an wasanni da tsofafin 'yan wasa ba suga karshen shekara 2016 ba, ciki har da Tsohon shugaban Fifa Joao Havelange wanda ya mutu yana dan shekara 100.

Ga Shu'iabu Amadu da Stephen Keshi da Tsohon dan wasan kwallon kafa na Ivory Coast Laurent Pokou da Tsohon dan wasan Italiya mai tsaron baya Cesare Maldini wanda ya mutu yana da shekara 84 da tsohon dan kwallon tawagar Netherland da Barcelona Johan Crupp da Dan wasan Dinamo Bucharest, Patrick Ekeng dan Kamaru wanda ya mutu bayan da ya fadi a cikin filin wasa a lokacin da yake yi wa kungiyarsa tamaula.

Da yake muna ban kwana da shekara ta 2016, ita ma 2017 za ta kunshi batutuwa da za a yi muhawara ko takaddama ko ce-ce-ku-ce ko jimami ko yin murna a fagen wasanni a duniya.