Wani kulob din China ya taya Ronaldo fam miliyan 250

rEAL mADRID
Bayanan hoto,

Ronaldo tare da Zidane kociyan Real Madrid

Mai kula da harkokin wasannin Cristiano Ronaldo, Jorge Mendes, ya ce wata kungiyar kwallon kafa a China ta yi wa Real Madrid tayin fam miliyan 250 domin ta dauki dan wasan Portugal.

Sai dai kuma Mendes ya ce Ronaldo mai shekara 31, bai yi shirin komawa can da murza-leda ba, duk da tayin albashin fam miliyan 85 da za a dunga ba shi a duk shekara.

Kudin da kungiyar ta China ta ce za ta bai wa Ronaldo a kowacce shekara zai kai naira 33,019,516,585:00.

A cikin watan Nuwamba ne Ronaldo ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da zama a Real Madrid zuwa Junin 2021, har ma ya ce zai iya kai wa shekara 10 a kungiyar.

Mendes ya ce "Kasuwar China sabuwa ce. Za su iya sayen 'yan kwallo da dama, amma ba zai yi wu Ronaldo ya koma can ba da murza-leda."

Ya kara da cewar "Ronaldo shi ne dan kwallon da ya fi fice a duniya. Saboda haka za a iya taya shi ko nawa ne."

Cikin yarjejeniyar da aka taya Ronaldo a China, zai karbi sama da fam miliyan 1.6 a kowanne mako, kan kwantiragin ninki uku kudin da aka sayi Paul Pogba daga Juvestus zuwa Manchester United kan kudi fam miliyan 89.