Serena Williams za ta auri Alexis Ohanian

Kwallon tennis

Asalin hoton, Reddit/AP

Bayanan hoto,

An dade ana ta rade-radin cewa Ohanian da Serena suna yin soyayya a boye

Fitacciyar 'yar wasan kwallon tennis, Serena Williams, ta yi amfani da kafar sada zumunta ta Reddit wajen sanar da baikonta tare da Alexis Ohanian.

Williams ta sanar da baikon da tayi da Ohanian daya daga cikin mamallakin Reddit ta hanyar rubutacciyar waka.

'Yar wasan tennis din ta ce ya gayyace ta Rome, birnin da suka fara haduwa, inda ya bukaci ta aure shi, kuma nan da nan ta amsa masa.

Shekara guda kenan a lokacin da Williams ta lashe kofin Wimbledon kuma babbar gasar tennis ta 22, koda yake yanzu ta koma mataki na biyu a jeren wadanda suke kan gaba a iya buga wasan.

Reddit wata kafar sada zumunta ce wadda al'umma ke tattauna batutuwa ko labarai ko yin muhawara, maimakon yin batun rayuwar mutanen da ba su san su ba a rayuwa.

Ohanian da Steve Huffman ne suka kafa shafin sada zumuntar na Reddit a shekara ta 2005.