Chelsea ta kafa tarihin cin wasannin Premier 13 a jere

Asalin hoton, AFP
Chelsea tana mataki na daya a kan teburi da maki 49
Chelsea ta kafa tarihin cin wasannin Premier 13 a jere a gasar bana, bayan da ta doke Stoke City da ci 4-2 a wasan mako na 19 da suka kara a ranar Asabar.
Chelsea ce ta fara cin kwallo ta hannun Gary Cahill a Stamford Bridge, sai dai kuma Stoke ta farke daf da za a je hutun rabin lokaci.
Bayan da aka dawo ne Willian ya ci wa Chelsea kwallo na biyu, ba a jima ba Peter Crouch ya buga tamaula ya wuce Thibaut Coutois ya fada raga.
Daga baya ne Willian ya kara na uku a ragar Stoke kuma na biyu da ya ci a fafatawar, kuma daf da za tashi ne Diego Costa ya ci na hudu kuma kwallo na 14 da ya ci a bana.
Chelsea ta yi kan-kan-kan tare da Arsenal a tarihin cin wasannin Premier 13, bayan da Arsenal ta fara kafa nata tarihin a kakar 2001/02.
Chelsea ta fara yin nasara a kan Hull City da ci 2-0 a ranar Asabar 1 ga watan Oktoban 2016, tun daga lokacin ne ta dunga lashe wasannin Premier da take yi.