United ta ci wasannin Premier biyar a Disamba

Gasar Premier mako na 19

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

United tana mataki na shida a kan teburin Premier da maki 36

Manchester United ta ci wasannin Premier biyar a jere a cikin watan Disamba a kakar Premier bana, bayan da ta doke Middlesbrough da ci 2-1 a Old Trafford a ranar Asabar.

Middlesbrough ce ta fara zura kwallo a ragar United ta hannun Grant Leadbitter bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci.

United ta farke kwallo ta hannun Anthony Martial kafin daga baya Paul Pogba ya ci mata na biyu, wanda hakan ya ba ta damar hada maki uku a karawar.

Da kuma wannan nasarar United ta ci wasannin Premier biyar a jere a watan Disambar 2016, wanda rabon da ta yi hakan tun a shekarar 2012.

Haka kuma kungiyar ta yi wasanni 10 kenan ba tare da an doke ta ba, ciki har da fafatawa takwas da ta yi a Old Trafford inda ta lashe gumurzu hudu da kuma yi canjaras sau hudu a gida.