Algeria ta ki gayyatar Feghouli kofin nahiyar Afirka

African cup of nations 2017

Asalin hoton, IAN KINGTON/GETTY IMAGE

Bayanan hoto,

Za a fara gasar cin kofin nahiyar Afirka a Gabon a ranar 14 ga watan Janairun 2015

Tawagar kwallon kafa ta Algeria ba ta bai wa Sofiane Feghouli, goron gayyata zuwa gasar cin kofin nahiyar Afirka da kasar za ta buga a Gabon a 2017 ba.

Tun farko an yi hasashen cewar kociyan Algeria, George Leekens, zai gayyaci Feghouli mai taka-leda a West Ham United zuwa gasar da za a fara a ranar 14 ga watan Janairu.

Sai dai kuma kociyan ya gayyato 'yan wasan kasar da suke buga tamaula a gasar Premier da suka hada da Riyad Mahrez da Islam Slimandi masu wasa a Leicester City da kuma Adlene Guedioura na Watford.

Algeria wadda take rukuni na biyu a gasar cin kofin nahiyar Afirka, za ka kara da Tunisia da Senela da kuma Zimbabwe.

Tawagar za ta fara wasan farko a ranar 15 ga watan Janairu a karawar da za ta yi da Zimbabwe a filin wasa da ke Libreville.

Ga jerin 'yan wasan da za su buga wa Algeria gasar cin kofin nahiyar Afirka:

Masu tsaron raga: Rais Ouhab M'bolhi (Antalyaspor, Turkey), Malik Asselah (JS Kabylie, Algeria), Chemseddine Rahmani (MO Bejaia, Algeria)

Masu tsaron baya: Mokhtar Belkhiter (Club Africain ,Tunisia), Mohamed Rabie Meftah (USM Alger, Algeria), Aissa Mandi (Real Betis, Spain), Hicham Belkaroui (Esperance, Tunisia), Liassine Cadamuro (Servette Geneva, Switzerland) , Mohamed Benyahia (USM Alger, Algeria), Ramy Bensebaïni (Stade Rennes, France), Faouzi Ghoulam (Napoli, Italy), Djamel Eddine Mesbah (FC Crotone ,Italy)

Masu buga tsakiya: Adlène Guedioura (Watford, England), Saphir Taïder (Bologna, Italy), Nabil Bentaleb (Schalke 04, Germany), Mehdi Abeid (Dijon, France), Yassin Brahimi (FC Porto, Portugal), Rachid Ghezzal (Olympique Lyon, France)

Masu cin kwallaye: Islam Slimani (Leicester City, England), Riyad Mahrez (Leicester City, England), Hilal Soudani El Arabi (Dinamo Zagreb, Croatia), Baghdad Bounedjah (Al Sadd, Qatar), Sofiane Hanni (Anderlecht, Belgium)