Liverpool ta ci gaba da zama ta biyu a kan teburin Premier

Gasar Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kwallo na biyu da Wijnaldum ya ci wa Liverpool a bana

Liverpool ta ci gaba da zama a mataki na biyu a kan teburin Premier, bayan da ta doke Manchester City 1-0 a wasan mako na 19 da suka fafata a Anfield a ranar Asabar.

Liverpool ta ci kwallon ne tilo ta hannun Georginio Wijnaldum a minti na takwas da fara tamaula, wanda hakan ya sa ta hada maki uku a karawar.

Da wannan nasarar Liverpool ta yi wasanni 17 a Anfield ba tare da an samu nasara a kanta ba.

Haka kuma kungiyar ta kafa tarihin hada maki 43 a wasanni 19 da ta buga a gasar Premier, bayan da ta taba hada maki 42 a kakar wasan 2008/09.

Liverpool za ta ziyarci Sunderland a wasan mako na 20, yayin da Manchester City za ta karbi bakuncin Burnley.