Bahagon Musan Kaduna ya buge bahagon Dogon Auta

Damben gargajiya
Bayanan hoto,

Damben da Bahagon Musan Kaduna ya buge Bahagon Dogon Auta

Bahagon Musan Kaduna ya buge Bahagon Dogon Auta a turfin farko a dambatawar da suka yi a gidan damben Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja a ranar Lahadi da safe.

Bahagon Musan Kaduna daga Arewa ya samu nasarar doke Bahagon Dogon Auta ne daga Kudu a turmi na biyu.

Shi kuwa Shagon Dan Shariff daga Kudu buge Yellon Gusau daga Arewa ya yi a turmin farko, Dan Aminu Shagon Langa-Langa kuwa Dogon Minista daga Kudu ya doke a turmin farko.

Sauran wasannin da aka yi canjaras ciki har da karawa tsakanin Bahagon Dan Samna'ila daga Kudu da Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa.

Shagon Mustapha daga Arewa da Bahagon Kugiya daga Kudu, da wasan Shagon Bahagon Mai Maciji daga Kudu da Shagon Inda daga Arewa.

Damben Shagon Ali Kwarin Ganuwa da Shagon Isa Kasa bai yi kisa ba, da wanda Shagon Bahagon Balan Gada daga Arewa da Shagon Autan Faya daga Kudu.