Dan Aminu Langa-Langa ya doke Dogon Minista a turmin farko

Dogon Minista ne ya bukaci Dan Aminun Langa-Langa su dambata a gidan damben Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja, Nigeria.

A cikin turmin farko Dan Aminu daga Arewa ya buge Dogon Minista daga Kudu, kuma wannan ne karon farko da suka taka dambe a tsakaninsu.

Mohammed Abdu ne ya hada labarin damben.