Swansea ta dauki Paul Clement koci

Derby County Paul Clement ya fara yi wa koci

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Swansea za ta kasance ta biyu da Paul Clement ya yi wa koci bayan Derby County

Mataimakin kocin Bayern Munich Paul Clement ya amince ya zama kocin kungiyar Swansea City tsawon shekara biyu da rabi.

Kungiyar wadda take matsayi na karshe a teburin Premier ta tattauna da kocin ne ranar Talata, bayan da Bayern Munich ta ba shi damar tattaunawar.

Kungiyar ta tattauna da Clement tun kafin nada Bob Bradley, wanda ta kora bayan rashin da aka doke ta a wasa 7 daga cikin 11, a matsayin kocinta a watan Oktoba.

Kocin mai shekara 44 ya zama kocinta na uku a kakar wasannin nan, kuma ana sa ran zai jagoranci kungiyar a wasan da za ta yi ranar Talata da Crystal Palace.

Tsohon mataimakin kocin Chelsea da Real Madrid ya rike Derby County tsawon wata 18 kafin kungiyar ta kore shi a watan Fabrairu na 2016.

Da ana ganin kungiyar za ta dauki wani daga cikin, wadannan; tsohon mataimakin kocin Manchester United Ryan Giggs da kocin Wales Chris Coleman da kuma tsohon kocin Birmingham City Gary Rowett.

Swansea ita ce ta karshe a tebur da maki 12 a wasanni 19, bayan da ta sha kashi a wasanninta hudu na karshe.