Sunderland ta yi wa Liverpool kancal da 2-2

Jermain Defoe

Jermain Defoe a lokacin da yake buga daya daga cikin fanareti biyun da Sunderlanda ta samu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jermain Defoe ya ci wa Sunderland kwallonta 11 daga cikin 19 a Premier bana

Sunderland ta rike bakinta Liverpool suka yi canjaras 2-2 a wasansu na mako na 20 na Premier.

Sau biyu da bugun fanareti Jermain Defoe yana farke wa Sunderlnad cin da Liverpool ta biyu a tebur ta yi mata.

Daniel Sturridge ne ya fara saka bakin a gaba da kwallon da ya ci a minti na 19, minti shida tsakani Defoe ya rama da fanareti, wadda alkalin wasa ya ba su saboda ketar da Ragnar Klavan ya yi wa Didier Ndong.

Can kuma a minti na 72 sai Mane ya kara ci wa Liverpool ta biyu, amma kuma Mane ya taba kwallon da hannu a da'irar gidansu, abin da ya sa alkalin wasa ya sake bayar da fanareti, wadda Defoe ya sake ci a minti na 84.

Sakamakon ya sa Liverpool mai maki 44 , ta rasa damar rage tazarar da ke tsakaninta da Chelsea ta daya a tebur mai maki 49, wadda za ta yi wasa a gidan Tottenham ranar Laraba.

Sunderland wadda ke cikin ukun karshe a tebur tana ta 18 da maki 15 a wasa 20