Man City ta zama ta 3 bayan ta doke Burnley 2-1

Fernandinho's third red card in six games for City means he will be banned for four matches and not available again until 5 February.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jan katin Fernandinho shi ne na biyu a Premier bana, abin da ya sa aka dakatar da shi wasa 4

Da 'yan wasa goma Manc City ta zama ta uku a tebur da maki 42, bayan ta doke Burnley 2-1 a Etihad a wasansu na mako na 20.

Clichy ne ya fara ci wa Manchester City kwallonta a minti na 58, kafin Agüero wanda ya shigo daga baya a ya kara ta biyu a minti na 62.

Mee ya rama wa bakin kwallo daya a minti na 70, abin da ya sa yanzu Burnley din ta zama ta 11 a tebur da maki 20 a wasa 20.

A kusan karshen lokacin farko ne na wasan alkalin wasa ya kori Fernandinho saboda ketar da ya yi wa Johan Gudmundsson, kafa bibbiyu.

Jan katin na Fernandinho, wanda shi ne na uku a wasa 6, na nufin za a hana shi wasa 4, wato ba zai dawo fili ba sai biyar ga watan Fabrairu.

Wannan shi ne karo na bakwai da ake ba wa Manchester City jan kati tun lokacin da Guardiola ya fara kocinta.

Ga sakamakon sauran wasannin na ranar Litinin:

Middlesbrough 0-0 Leicester City;

Har yanzu Leicester, ba ta ci wasa ba a waje a Premier bana, sabanin 11 da ta ci a bara da ta dauki kofi.

Middlesbrough tana matsayi na 16 da maki 19, yayin da Zakarun Premier suke matsayi na 14 da maki 21.

Everton 3-0 Southampton;

Everton ta zama ta bakwai da maki 30 yayin da Southamtpton ta zama ta goma da maki 24.

West Bromwich 3-1 Hull City;

West Brom ta zama ta takwas a tebur da maki 29, yayin da Hull take ta 19 da maki 13, maki uku tsakaninta da faduwa daga gasar Premier.