Man United ta ci West Ham 2-0, amma tana matsayinta

Juan Mata kenan a lokacin da ya ci West Ham kwallon farko

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Juan Mata kenan a lokacin da ya ci West Ham kwallon farko

Manchester United ta bi West Ham har gida ta doke ta da ci 2-0 a wasan Premier na mako na 20, amma duk da nasarar tana matsayinta na shida.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne Juan Mata ya ci wa United kwallonta ta farko a minti na 63.

Sai kuma Ibrahimovic daya daga cikin 'yan wasan United uku da ake ganin sun yi satar gida, ya kara ta biyu a minti na 78.

Duk da wannan nasara Man United tana matsayi na 6 da maki 39, saboda Tottenham wadda take ta biyar tana da maki 39, amma da yawan kwallo 23, United tana da kwallo 10.

Nasara ta shida a jere da Jose Mourinho ya samu kenan a wasannin Premier kuma ta bakwai a dukkanin wasannin da suke yi a bana.

Ita kuwa West Ham ta yo kasa zuwa matsayi na 13 daga na 12, inda take da maki 22 a wasa 20.

A ranar Laraba ne Chelsea ta daya a tebur da maki 49 za ta fafata da Tottenham a wasansu na mako na 20.