Guardiola: Na kusa barin aiki

Guardiola ya ce Man City na iya zama daya daga kungiyoyinsa na karshe

Asalin hoton, AFP Getty

Bayanan hoto,

Guardiola ya ce ya fara shirin ajiye aikin koci

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce ya fara shirin kawo karshen aikinsa na koci, domin ba zai ci gaba da aikin ba idan ya kai shekara 60 ko 65

Kocin mai shekara 45, dan Spaniya ya horar da kungiyar Barcelona da Bayern kafin ya maye gurbin Manuel Pellegrini a Manchester City a bazarar da ta gabata.

Kocin ya ce, kila zai kasance a Manchester tsawon kaka uku nan gaba, kamar yadda ya fada a wata hira kafin wasansu da Burnley na Litinin.

Kocin ya jaddada matsayin nasa da cewa ba shakka ya kama hanyar karshen aikinsa na horarwa.

Guardiola ya dauki kofi 14 a shekara hudu da ya yi da Barcelona, wadanda suka hada da na La Liga uku da na Zakarun Turai biyu.

Ya yi hutun shekara daya bayan barinsa Barcelona kafin ya koma Bayern Munich a 2013, inda ya jagorance su, suka dauki kofin Bundesliga uku a jere, amma kuma bai iya cin kocin Zakarun Turai da Zakarun na Jamus ba.

Guardiola ya ce, ba zai cigaba da zama a benci ba har zuwa shekara 60 ko 65 ba, kuma yana ganin tuni ya kama hanyar sallama da aikin koci,