Wenger: An nuna bambanci a Premier

Wasannin Arsenal uku na lokacin hutu a cikin kwana tara ne, wanda ta fi na Liverpool da kwana biyu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wenger: "A shekara 20 ban taba ganin irin wannan bambancin ba''

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya koka da yadda aka tsara wasannin lokacin hutun Kirsimeti da sabuwar shekara, da cewa a shekara 20 bai taba ganin wanda ba a yi raba daidai ba kamarsa.

Wenger ya ce lokacin hutu tsakanin wasa da wasa ya bambanta fiye da tsammani, idan aka kwatanta da wasu kungiyoyin.

A ranar Talata Arsenal za ta je gidan Bournemouth, bayan da ta ci Crystal Palace ranar Lahadi, yayin da Chelsea ta daya a tebur wadda ta ci wasanta ranar Asabar ba za ta yi wasa ba sai ranar Laraba a gidan Tottenham.

Nasarar da Arsenal ta yi a kan Crystal Palace ta ba wa Gunners din damar zuwa matsayi na uku, amma da maki tara tsakaninsu da Chelsea, kafin wasansu da Bournemouth ta tara a tebur ranar Talata.

Kocin ya ce: ''Ba wasan da za a ce ba shi da wahala a wannan gasar ta Premier, inda a yanzu za mu yi wani wasan cikin sa'a 48."

A duk tsawon lokacin hutun, Arsenal ce za ta samu hutu a tsakanin wasanninta uku, fiyea da dukkanin sauran abokan hamayyarta hudu, in ban da Chelsea, inda Liverpol kuma take da kwana uku na hutu idan aka kwatanta da kungiyar ta Antonio Conte.

Chelsea, wadda ta doke Bournemouth ranar 26 Disamba, kuma ta ci Stoke ranar 31 ga watan Disamba, za ta kammala wasanninta na lokacin hutun ranar Laraba a gidan Tottenham.

'Yan wasan Southampton su ne suka fi karancin hutu tsakanin wasanninsu, kuma sun yi rashin nasara a dukkanin wasannin uku.