Klopp: Na ba wa 'yan wasana damar hutu, amma sun ki

Mai sharhi kan wasannin Premier Martin Keown ya ce: "Shi kansa Klopp yana da alamun gajiya."
Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce ya ba wa 'yan wasansa damar barin su su huta a wasansu da Sunderland ranar Litinin, idan sun gaji sosai, amma ba wanda ya ce ya gaji ba zai iya ba.
Liverpool din ta yi canjaras 2-2 a gidan Sunderland, kasa da sa'o'i 44 bayan ta doke abokan hamayyarta Manchester City.
Klopp ya ce: "Na tambayi 'yan wasan idan akwai wanda ba zai iya wasan ba, kuma na tabbatar musu cewa ba wanda zan gayawa, amma kuma ba wanda ya fito fili ya amsa. Wannan kyakkyawan abu ne.''
Mai sharhi kan wasannin Premier Martin Keown ya ce: "Shi kansa Klopp yana da alamun gajiya."
Canjaras din ta sa Liverpool maki biyar a bayan jagorar gasar Chelsea, wadda za ta je gidan Tottenham ranar Laraba da karfe 9 na dare agogon GMT.
A yayin wasan 'yan Liverpool sun yi zirga-zirgar da ta kai ta jumullar kilomita 118.63, inda suka fi 'yan Sunderland,wadanda suka ci kilomita 115.89.
Hakan ya zo daidai da yadda suka yi a sauran wasanninsu na lokacin hutun nan, inda suka yi gudun kilomita 116.87 a lokacin da suka doke Manchester City.
Da kuma kilomita 118.94 da suka ci a wasan da suka buge Stoke 4-1 ranar 27 ga watan Disamba.