FA ta tuhumi Bacary Sagna

Kocin Burnley na ganin kamat ya yi ma a ba wa Sagna katin kora

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An ba wa Sagna katin gargadi saboda taka George Boyd da ya yi bayan kwallon da Burnley ta ci

Hukumar kwallon kafa ta Ingila, ta nemi dan wasan Manchester City Bacary Sagna ya yi bayani kan abin da yake nufi da rubutun da ya sanya a shafinsa na Instagram na ''10 da 12'' ( "10 against 12"), wanda ya saka bayan wasan da suka ci Burnley 2-1 ranar Litinin.

'Yan Manchester City sun ragu da mutum daya bayan da alkalin wasa Lee Mason ya kori Fernandinho a minti na 32 da wasa.

Sagna ya goge rubutun da ake maganar a kan shi daga shafin nasa, amma FA, ta tuntubi dan wasan na baya da ya yi mata bayanin abin da yake nufi da shi.

Dan wasan dan Faransa yana da wa'adin har zuwa karfe biyar na yamma agogon GMT ranar Juma'a ya bayar da bahasin.