Wariyar launin fata: Kotu ta yanke wa 'yan Chelsea hukunci

James Fairbairn (hagu) da Joshua Parsons sun halarci zaman kotun

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

James Fairbairn (hagu) da Joshua Parsons sun halarci zaman kotun

Wata kotu a Faransa ta yanke wa wasu magoya bayan Chelsea 4 da aka zarga da laifin cin zarafin wani bakar fata, da nuna bambancin launin fata hukuncin zaman gidan yari na shekara daya da tarar Euro dubu 10.

Sai dai hukuncin dagagge ne wanda sai idan an same su da wani laifin a nan gaba za a aiwatar da shi.

A lokacin zaman shari'ar biyu daga cikin mutanen sun ce abin da suka yi na hana bakar fatar shiga jirgin kasa a wata tashar jirgi a Paris a watan Fabrairu na 2015, ba shi da nasaba da bambancin launin fata, kamar yadda ake zarginsu.

Sauran biyun an yi musu shari'ar ne a bayan idonsu domin ba su halarci zaman kotun ba.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Souleymane Sylla, ya bayyana lamarin a matsayin abin da ya kunyata shi

Kotun ta kuma umarce su da su biya mutumin, Souleymane Sylla, wanda dan Faransa ne asalin kasar Mauritania, wanda suka ci wa zarafin euro dubu goma.

Mutanen sun ci zarafin sa ne a lokacin da za su je kallon wasan cin kofin Zakarun Turai tsakanin kungiyarsu Chelsea da Paris Saint-Germain.

Asalin hoton, COURT HANDOUT

Bayanan hoto,

An dauki hoton bidiyon abin da ya faru a lokacin

Daman tuni Chelsea ta haramta musu halartar wasanninta har abada, yayin da wata kotun majistare a Ingila ta haramta musu halartar manyan wasannin kwallon kafa tsawon shekara biyar.

Kocin kungiyar a lokacin Jose Mourinho, ya bayar da hakuri tare da nuna nadama a kan abin da magoya bayan kungiyar tasa suka yi.