Conte: Chelsea za ta sayo 'yan wasa

Saura nasara a wasa biyu kungiyar ta Conte ta kafa tarihi a Ingila

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Saura nasara biyu Chelsea ta kafa tarihi a kwallon kafar Ingila

Kocin Chelsea Antonio Conte ya ce kila ya kara karfin kungiyarsa da wasu sabbin 'yan wasa idan aka bude kasuwar saye da sayar da 'yan wasa a watan nan na Janairu domin ya kara damarsa ta daukar Premier.

Jagorar ta Premier tana neman kafa tarihin nasara a jere a wasa 14 a kaka daya, idan suka je gidan Tottenham ranar Laraba.

Idan ta yi nasara a wasan da Tottenham za ta kara yi wa Liverpool ta biyu a tebur tazara da maki takwas.

Kocin ya ce, akwai wuraren da idan muka samu 'yan wasan da suka dace da su, yana da kyau mu sayo su.

Chelsea ta doke Tottenham 2-1 a Stamford Bridge a watan Nuwamba, a kan hanyarta ta kafa tarihi irin na Arsenal na yin nasara a wasa 13 na Premier a jere.

Idan kungiyar ta yi nasara a kan Tottenham a ranar Laraba, za ta zama ta farko a tarihi da ta ci wasa 14 a jere a gasar Premier a kaka daya.

Sannan kuma idan har suka yi nasara a gidan Leicester a wasansu na gaba, hakn zai sa su kafa tarihi na yin nasara 15 a jere a wasan kwallon kafa na Ingila.