Arsenal ta tsira a Bournemouth 3-3

Giroud ne kanwa uwar-gami a dukkanin kwallayen da Arsenal ta ci Bournemouth

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Giroud ne ya rama wa Arsenal ta uku, kuma yana da hannu a duk ukun da ta ci Bournemouth

Arsenal ta tsira daga ci uku da Bournemouth ta yi mata suka tashi canjaras 3-3 a wasan Premier na mako 20, sai dai kungiyoyin sun ci gaba da zama a matsayinsu a tebur.

Sakamakon ya sa Arsenal ta uku a tebur yanzu ta ci gaba da zama a matsayin amma da maki 41, yayin da Bournemouth ta ci gaba da zama a matsayinta na tara da maki 25.

Daniels ne ya fara cin Arsenal a minti na 16, kafin kuma Wilson ya ci ta biyu da bugun fanareti a minti na 20.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne kuma Fraser ya kara cin bakin kwallo ta uku a minti na 58.

Minti goma sha biyu tsakani ne kuma sai Sanchez ya rama wa Gunners kwallo daya.

Kwallon ta ba wa Arsenal kwarin guiwa, abin da ya sa nan da nan minti biyar tsakani Perez ya samu damar kara ta biyu a ragar Bournemouth.

Ana daidai da tashi ne bayan minti biyu cikin karin lokacin da aka bata sai Giroud ya farke kwallo ta uku.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

A ranar Laraba ne Tottenham ta biyar a tebur da maki 39, za ta karbi bakuncin Chelsea ta daya da maki 49.

Idan har Chelsea ta yi nasara za ta kara rata a matsayinta na daya da maki 52.

In kuwa suka yi canjaras Chelsea za ta kara zama a matsayin da maki 50, ita ma Tottenham za ta ci gaba da zama ta biyar amma da maki 40, daya kenan tsakaninta da Arsenal.

In kuma Tottenham ta doke Chelsean za ta iya tsallakewa ta kawar da Manchester City daga matsayi na uku, inda za ta kasance da yawan maki daya da City, wato 42, amma da bambancin yawan kwallo.

Idan hakan ta kasance Manchester City kenan za ta dawo ta hudu, yayin da Arsenal za ta yo kasa zuwa matsayi na biyar.

Ga sakamakon sauran wasannin na Premier na ranar Talata:

Swansea ta karshe a tebur ta bi Crystal Palace gida ta doke ta 2-1, inda ta dago zuwa ta biyun karshe da maki 15, yayin da Palace din ta kasance ta 17 da maki 16.

Stoke City a gidanta ta ci Watford 2-0, abin da ya sa ta kawo karshen wasanninta biyar ba nasara.

Yanzu ta haura bakin nata a tebur ta zama ta 11 da maki 24, yayin da Watford ta kasance ta 14 da maki 22.