Chapecoense za ta dauko sabbin 'yan wasa 20

Asalin hoton, Reuters
Magoya bayan kungiyar Chapecoense yayin jimamin hadarin a filin wasan kungiyar
Kungiyar Chapecoense ta Brazil za ta dauko sabbin 'yan wasa guda 20 domin kaka ta gaba, kuma ta ajiye lambobin rigunan 'yan wasan da suka tsira a hadarin jirgin saman da tawagarta ta yi.
'yan wasa 19 da masu horar da su ne suka mutu a hadarin jirgin saman da tawagar ta yi a watan Nuwamba, a lokacin da take kan hanyarta ta wasan karshe ta kofin Latin Amurka (Copa Sudamericana).
An dai bai wa kungiyar kofin, yayin da abokan karawarsu Atletico Nacional 'yan Colombia suka samu kyautar wasa da lumana.
Darektan kwallon kafa na kungiyar Rui Costa ya ce: "Za mu dauki aron 'yan wasa da dama."
"Wannan ita ce hanyar hada nagarta da kuzari da kuma kasafi. Kuma kungiyoyi da dama na hada hannu da mu a wannan kudiri."
Costa ya ce suna sa ran 'yan wasansu na baya Neto da Alan Ruschel da suka tsira a hadarin, su dawo su sanya rigunansu na wasa.
Mai tsaron ragarsu na wucin-gadi Jackson Follmann, shi ma ya tsira, amma kuma an yanke masa wani sashe na kafarsa.
Costa ya ce golan zai ci gaba da kasancewa da kungiyar a wani matsayi.
Darektan ya ce, ba wani dan wasa da zai sanya rigunan 'yan wasan da suka tsira a hadarin.
Kungiyar ta Chapecoense, wadda ta fara atisayen shirin tunkarar sabuwar kaka ranar Juma'a, za ta fara wasannin gasar kasar ranar 26 ga watan Janairu a gidanta da kungiyar Joinville.
Kungiyar ta ki amincewa da wani tsari da aka gabatar mata wanda zai kare ta daga faduwa daga gasar kasar tsawon shekara uku.