Kofin FA: Mike Dean zai jagoranci wasa duk da sukar da yake sha

Mike Dean a wani hukunci da ya yi
Bayanan hoto,

Mike Dean na shan suka kan hukunce-hukuncensa a wasanni

Alkalin wasa Mike Dean zai jagoranci wasan cin kofin kalubale na hukumar kwallon kafa ta Ingila, FA, na zagaye na uku tsakanin Tottenham da Aston Villa - duk da sukar da ake masa kan salon alkalancinsa.

Kocin West Ham Slaven Bilic ya soki dalilin Dean na korar Sofiane Feghouli a wasan da Manchester United ta ci su 2-0 ranar Litinin.

Wannan shi ne jan kati na biyar da alkalin wasan ya bayar a wasanni goma sha biyar a bana.

West Ham ta daukaka kara kan jan katin da Dean ya ba wa dan wasan na Faransa bayan minti 15 da wasa a sanadin karonsu da Phil Jones, abin da koci Bilic yake ganin dan bayan United din ne ma ya fi aikata laifi.

Korar dan wasan ita ce ta 25 da Dean ya yi tun da aka fara kakar wasa ta 2013-14, wanda hakan ya sa ya fi duk wani alkalin wasa na Premier na yanzu yawan kora a bana.

Masu fashin-bakin wasan kwallon kafa da dama na sukar alkalin wasan kan yadda yake yawan korar 'yan wasa da kuma sauran hukunce-hukunce da yake yi.