Bournemouth za ta daukaka kara kan jan katin Francis

Alkalin wasa Michael Oliver, yana ba wa Francis jan kati

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Alkalin wasa ya ba wa Francis jan katin kai tsaye saboda ketar da ya yi wa Aaron Ramsey

Bournemouth za ta daukaka kara a kan jan katin da aka ba wa Simon Francis a wasan da suka yi canjaras 3-3 da Arsenal ranar Talata.

Alkalin wasa ya kori dan wasan baya Francis, mai shekara 31, kan yadda ya kalubalanci Aaron Ramsey,a karon da Gunners din suka farfado daga 3-0 suka farke kwallayen duka.

Kocin Bournemouth Eddie Howe ya ce hukuncin da alkalin wasa Michael Oliver ya yi na korar Francis kafin Giroud ya rama kwallo ta uku, ya yi tsauri.

Howe ya ce, laifi ne ba shakka amma ba ya jin ya kai har a kore shi.

Zuwa karshen makon nan kungiyar ke sa ran jin sakamakon daukaka karar, wadda idan ba ta yi nasara ba, Francis ba zai yi wasan ranar Asabar ba na kofin FA na zagaye na uku da Millwall.

Haka kuma ba zai buga wasan da Bournemouth din za ta yi ba na Premier da Hull City da kuma Watford.