'Kocin Portugal ne ya dace da Hull City'

Asalin hoton, Reuters
A ranar Litinin Phelan ya jagoranci Hull City a wasan da West Brom ta doke ta 1-0
Kocin Portugal Marco Silva ya zama na gaba-gaba da masu fashin bakin wasan kwallon kafa ke gani ya cancanci maye gurbin tsohon kocin Hull City Mike Phelan wanda ta kora ranar Talata.
A kakar da ta wuce Silva ya horar da Olympiacos kafin ya bar kungiyar a lokacin bazara. Haka shi ma tsohon kocin Birmingham Gary Rowett yana daga cikin wadanda ake ganin sun cancanta a ba su mukamin.
Sai dai tsohon kyaftin din Hull Cityn Ian Ashbee, wanda sun yi wasa tare da Rowett, ba ya jin tsohon abokin wasan nasa zai karbi aikin, idan an ba shi.
Phelan, mai shekara 54, ya karbi aikin ne a matsayin kocin rikon-kwarya sakamakon tafiyar Steve Bruce a lokacin bazara.
Sannan kuma ya zama kocin Hull din na dindindin a watan Oktoba.
Amma kasancewar kungiyar tana cikin rukunin faduwa daga Premier, inda ta samu maki uku a wasanninta tara, sai ta sanar da sallamar Phelan.
Kungiyar ta ce nan ba da jimawa ba za ta sanar da magajinsa.
Shi dai Phelan ya fara aikin kocin kungiyar da sa'a, inda har ya samu kyautar kocin Premier da ya fi kwazo na watan Agusta.
To amma kuma sai lamarin ya sauya daga baya, ya kasance rabon da kungiyar ta ci wasa tun ranar 6 ga watan Nuwamba, lokacin da ta ci Southampton 2-1.
Nasarar da Swansea ta yi a kan Crystal Palace ranar Talata, ta sa Hull ta zama ta karshe a teburin Premier, maki uku tsakaninta da faduwa.
Phelan wanda tsohon mataimakin kocin Manchester United ne ya jagoranci Hull tsawon kwana 85 a matsayin kocinta, kari da wasu kwanakin 81 na rikon kwarya.