Middlesbrough ta sayi Rudy Gestede

A bana Rudy Gestede ya ci kwallo hudu ne kawai a wasa 19.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A bana Rudy Gestede ya ci kwallo hudu ne kawai a wasa 19.

Middlesbrough ta dauki dan wasan tawagar Jamhuriyar Benin Rudy Gestede daga kungiyar Aston Villa da ke wasa a rukunin kasa da Premier na 'yan dagaji (Championship).

Rahotanni sun ce kungiyar da ke fafutukar ganin ba ta fadi ba daga gasar ta Premier ta sayo dan wasan ne a kan fan miliyan shida.

Gestede mai shekara 28 wanda ya fara taka leda a Ingila a kungiyar Cardiff a 2011, ya kulla yarjejeniyar shekara uku ne da Middlesbrough.

Kuma zuwansa kungiyar zai bayar da damar tafiyar wasu 'yan wasan gaban, Jordan Rhodes da David Nugent.

Sai dai a sanarwar da ita kungiyar ta sanya kan sayen dan wasan a shafinta na intanet, ba ta bayyana yawan kudin da ta saye shi ba.

Dan wasan haihuwar Faransa, bai yi kokari ba sosai a Aston Villa, inda ya ci kwallo biyar kawai a wasan Premier 24, a bara lokacin da suka fadi daga Premier.

A bana tsohon dan wasan tawagar Faransa ta 'yan kasa da shekara 19 ya ci kwallo hudu ne a wasa 19.

Amma kuma kocinsu Steve Bruce ya ajiye shi a benci, bayan da ya maye gurbin Roberto di Matteo a matsayin kocin kungiyar ta Aston Villa.