Haramcin Fernandinho na wasa 4 ya tabbata

Jan katin Fernandinho a wasansu da Burnley shi ne na biyu a Premier bana

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jan katin Fernandinho a wasansu da Burnley shi ne na biyu a Premier bana

Manchester City ta yi rashin nasara a karar da ta daukaka ta neman soke hukuncin kora na jan kati da aka ba dan wasanta Fernandinho, na haramcin wasa hudu.

Alkalin wasa ya kori dan wasan na tsakiya mai shekara 31, saboda ketar da ya yi wa dan wasan Burnley Johann Berg Gudmundsson, kafa bibbiyu ranar 2 ga watan Janairu, wanda hakan ya kasance jan kati na uku da aka ba shi a bana.

Kasancewar hukumar kwallon kafa ta Ingila ta yi watsi da daukaka karar, hukuncinsa na haramcin buga wasa hudu zai fara ne daga yanzu.

Dan wasan na Brazil ba zai yi wasan cin kofin FA na ranar Juma'a na zagaye na uku da West Ham.

Sannan kuma ba zai buga wasan Manchester City din na Premier da Everton da Tottenham da kuma West Ham ba.