Sunderland ta ki tayin West Ham na fan miliyan 6 kan Defoe

Jermain Defoe a lokacin da yake cin Liverpool a wasan da suka yi 2-2 na Premier bana

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Jermain Defoe ne ya ci wa Sunderland kwallonta biyu da suka yi 2-2 da Liverpool ranar Litinin

Sunderland ta yi watsi da tayin da West Ham ta yi kan dan wasanta na gaba Jermain Defoe na fan miliyan shida.

Sai dai ana ganin Sunderland din za ta kara farashin dan wasan, wanda ya fara wasansa na kwararru a kungiyar ta gabashin Landan.

Defoe, mai shekara 34, ya ci kwallo 11 a wasanni 21 da ya yi wa kungiyar da ke fafutukar neman tsira daga faduwa daga Premier a bana.

Kwallonsa ta baya-bayan nan ita ce ta ranar Litinin, lokacin da sau biyu Sunderland ta yunkuro ta rama cin da Liverpool ta yi mata, suka yi 2-2.

A sakamakon canjaras kungiyar ta David Moyes ta zama ta 18 a teburin Premier.

Defoe ya fara wasansa ne na babbar kungiya a West Ham kafin Tottenham ta saye shi fan miliyan bakwai a 2004.

Cinikin da ita kuma West Ham ta karbi Bobby Zamora daga Tottenham.

A watan Janairu na 2008 ne kuma Portsmouth ta saye shi kan fan milina 7.5 kafin ya sake dawowa Tottenham a 2009 a kan fan miliyan 15.

Ba zato ba tsammani Defoe ya tafi kungiyar Toronto FC ta Canada a 2014, kafin tsohon kocin Sunderland Gus Poyet ya sake dawo da shi a 2015.