West Ham ta yi nasarar janye jan katin Feghouli

West Ham ta yi wasan minti 75 da 'yan wasa 10 bayan da aka kori Sofiane Feghouli kan haduwarsu da Phil Jones

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

West Ham ta yi wasan minti 75 da mutum 10 bayan da aka kori Sofiane Feghouli kan yadda ya yi wa Phil Jones

West Ham ta yi nasara a karar da ta daukaka kan jan katin kora da alkalin wasa ya ba wa Sofiane Feghouli a wasanta da Manchester United ranar Juma'a.

A sakamakon wannan hukunci da hukumar kwallon kafa ta Ingila FA, ta yanke, dan wasan zai buga wasan West Ham za ta yi na cin kofin kalubale na FA din da Manchester City ranar Juma'a

Alkalin wasa Mike Dean, wanda ake ta cece-ku-ce kan yadda yake jagorantar wasa ne, ya ba wa dan wasan dan Aljeriya, mai shekara 27 jan kati kai tsaye kan yadda ya tunkari Phil Jones, a minti 15 da fara wasan na Premier na ranar Litinin.

Manchester United ce ta yi nasara a wasan da ci biyu ba ko daya bayan an dawo daga hutun rabin lokacin.

A wani sako da mataimakin shugaban kungiyar ta West Ham Karren Brady ya sanya a shafin Tweeter, kan hukuncin ya ce, ba dade wa aka kira shi ta waya aka tabbatar masa cewa Sofiane ba zai yi hukuncin kauracewa wasa uku ba, kuma yana da damar buga wasansu na ranar Juma'a

Feghouli, wanda ke wasanninsa na farko a Premier tun lokacin da ya je West

Ham daga Valencia ta Spaniya, bayan da kwantiraginsa ta kare, yana da damar yi wa kungiyar wasanninta na Premier na gaba.

Wasannin da za ta yi da Crystal Palace da Middlesbrough.

Yanzu dai hankali zai karkata ne kan alkalin wasa Dean lokacin da zai jagorancin wasan zagaye na uku na cin kofin FA tsakanin Tottenham da Aston Villa ranar Lahadi