Cin hanci: Za a tuhumi Issa Hayatou a Masar

Asalin hoton, Getty Images
Issa Hayatou ya taba rikon kwarya na Fifa lokacin da aka haramta wa tsohon shugabanta Sepp Blatter shugabancin
An umarci babban mai gabatar da kara na Masar ya tuhumi shugaban hukumar kwallon kafar Afirka CAF, Issa Hayatou , kan zargin cin hanci.
Hukumomin Masar sun gabatar da tuhumar ne saboda hedikwatar hukumar kwallon ta Afirka tana babban birnin kasar ne Alkahira.
Hukumomin suna zargin cewa lokacin da CAF ta kulla wata yarjejeniyar watsa wasannin gasar Afirka da kamfanin wasanni na Faransa Lagardere, ba a bi dokokin kasar da suka bukaci a ba kowane kamfani damar neman kwangilar ba tare da nuna bambanci ba.
D aka tuntubi hukumar ta kwallon kafar Afirkan ta ki ta ce komai kan lamarin.
Babban Labari
Minti Daya Da BBC
Saurari, Minti Daya Da BBC Safe 18/01/2021, Tsawon lokaci 1,00
Minti Daya Da BBC Safe 18/01/2021