Tottenham ta taka wa Chelsea birki da 2-0

Daya daga cikin kwallo biyun da Alli ya ci Chelsea

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kwallon Dele Alli ta 9 da ta 10 a Premier sun taka wa Chelsea birki

Tottenham ta kawo karshen nasarar da Chelsea ke yi har 13 a jere a wasan Premier bayan da ta doke ta 2-0, kuma ta tsallaka daga ta biyar zuwa ta uku a tebur da maki 42.

Nasarar dai ta fi cutar da Arsenal a kan Chelsean, domin Tottenham din ta kado Gunners din daga matsayi na hudu suka dawo na biyar da maki 41.

Yayin da Manchester City ita ma ta yo kasa zuwa mataki na hudu da maki 42 amma da bambancin kwallo 6 tsakaninta da Tottenham.

Har yanzu Chelsean tana matsayi na daya da maki 49, yayin da Liverpool ke cigaba da zama ta biyu da maki 44.

Dele Alli ne ya ci wa Tottenham kwallonta biyu, ta farko a minti daya da cikar minti 45 na farkon wasa.

Sannan ya ci ta biyu bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a minti na 54.

Yanzu Dele Alli ya ci kwallo 7 a wasanninsa 4 na Premier na baya bayan nan.

A bana ba a doke Tottenham ba a gidanta, inda ta ci wasa 8, kuma ta yi canjaras a guda 2, tarihin da ba ta taba kafawa ba na kasa doke ta a gida tun kakar 2000/01, da ta kai har wasa 13.

Rabon da Chelsea ta yi nasara a gidan Tottenham, White Hart Lane, tun a watan Oktoba na 2012 lokacin da ta ci su 4-2, kuma tun daga lokacin sun yi canjaras sau 2, Tottenham ta ci ta sau 2.