China za ta hana kashe makudan kudade kan 'yan wasan waje

Shanghai Shenhua ta sayo Carlos Tevez daga Boca Juniors ta Argentina

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Komawar Carlos Tevez China ya zama dan wasan da ya fi samun albashi mai yawa a duniya

Hukumomin China za su hana kungiyoyin kwallon kafa na kasarsu kashe makudan kudade kan 'yan wasan kwallon kafa na duniya.

A wata hira da aka watsa bayaninta wadda wani mai magana da yawun gwamnatin kasar wanda ba a fadi sunansa ba, ya yi, hukumomin suka bayyana matakin.

Sun ce za su takaita yadda kungiyoyin ke sayowa tare da biyan albashi na kudade masu yawan gaske ga fitattun 'yan wasa na waje.

Hukumomin na China sun bayyana wannan matakin ne 'yan kwanaki bayan da kungiyar Shanghai SIPG ta sayi dan wasan Brazil Oscar daga Chelsea a kan dala miliyan 63, cinikin da ya zarta na duk wani dan wasa da aka taba yi a nahiyar Asia.

Haka shi ma tsohon dan wasan Manchester United da Manchester City, Carlos Tevez na Argentina, kungiyar Shanghai Shenhua da ke hammayya da SIPG, ta sayo shi a kan kudin da aka ce ya kai euro miliyan 84.

Kuma kamar yadda rahotanni suka bayyana zai kasance dan wasan da ya fi daukar albashi mai yawa a duniya, inda za a rika biyansa fan 615,000 a duk mako ko euro miliyan 38 a duk shekara, tsawon shekara biyu.

Shi kuwa Oscar ana ganin SIPG za ta rika biyansa albashin euro miliyan 24 a shekara, wanda hakan ya zarta na Cristiano Ronaldo da Lionel Messi.

A shekarar da ta wuce ta 2016 sau hudu kungiyoyin kwallon kafa na China suna kafa tarihi na sayen 'yan wasa a ciniki mafi tsada a duniya, inda suka zarta hatta Premier Ingila da ake kashe makudan kudade.

A watan Disamba hukumar kwallon kafa ta China ta ce za ta rage yawan 'yan wasa na kasashen waje a gasar kasar a kungiyoyi daga biyar zuwa biyu.

China dai ita ce ta 82 a jerin hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, na kasashen da suka fi iya taka leda a duniya.