Arsenal ta sayo wani matashin dan wasa Cohen Bramall

Cohen Bramall a wani wasan Hednesford

Asalin hoton, Express and Star

Bayanan hoto,

Cohen Bramall ya fara wasansa a cibiyar matasan 'yan wasa ta Nantwich Town, kuma ya yi kananan kungiyoyi da yawa kafin ya tafi Hednesford

Arsenal ta sayo matashin dan wasan baya na wata karamar kungiya Hednesford Town, Cohen Bramall, dan shekara 20, a kan fan dubu 40.

Dan wasan ya biyo layin da Ashley Williams na Everton ya bi, wanda shi ma ya faro wasansa daga kungiyar ta Hednesford.

Rahotanni sun ce Crystal Palace da Sheffield Wednesday dukkanninsu sun duba Bramall, amma Arsenal ce kawai ta yi nasarar sayensa.

Dan wasan wanda ya fito daga yankin South Cheshire a Ingila, cikakken ma'aikaci ne a masana'antar hada motar Bentely da ke Crewe, kafin a sallame shi a wani mataki na rage ma'aikata.

Daga nan ne kuma sai ya samu aiki a wani shagon sayar da tufafi.