Koci: Hull City ta dauki Marco Silva

Marco Silva ya yi manyan wasanni biyu ne kawai a tawagar Portugal ta kasa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Silva zai jagoranci Hull tana karshen tebur, maki uku tsakaninta da tsira

Hull City ta tabbatar da daukar tsohon kocin Olympiakos Marco Silva a matsayin sabon kocinta, domin maye gurbin Mike Phelan wanda ta kora.

Kocin dan Portugal mai shekara 39ya kulla yarjejeniya da kungiyar har zuwa karshen kakar wasannin da ake ciki.

Silva ya maye gurbin Mike Phelan wanda kungiyar ta karo ranar Talata, yayin da kungiyar take karshen teburin Premier.

A lokacin bazara ne ya bar Olympiakos, kuma a da ana ganin zai tafi tsakanin kungiyar Wolves ne ko Nottingham Forest.

A ranar Asabar ne zai jagoranci Hull a wasan da za ta yi da Swansea wadda ita ma ke neman faduwa daga Premier, a wasan zagaye na uku na kofin FA.

Kocin wanda tsohon dan baya ne, ya fara horarwa a 2011 da kungiyar Estoril ta rukuni na 2 a Portugal, wadda kusan a ita ya yi yawancin wasansa.

Ya jagoranci kungiyar ta cigaba zuwa babbar gasar Portugal, da kuma kai ta gasar kofin Europa, kafin ya koma Sporting Lisbon a 2014.

A lokacinsa ne Sporting ta ci kofin kalubale na Portugal, amma kuma kungiyar ta kore shi a watan Yuni na 2015 kawana hudu da daukar kofin.

Rahotanni sun ce an kore shi ne saboda ya ki sanya rigar kwat ta kungiyar a lokacin wani wasansu na cin kofin.

Ya kulla yarjejeniyar shekara biyu da Olympiakos wata daya bayan sallamarsa, kuma kungiyar ta Girka ta kafa tarihin cin wasan gasar kasar 17 a jere a lokacinsa.

Sannan kuma ya jagoranci kungiyar ta doke Arsenal 3-2 a Emirates a gasar cin Kofin Zakarun Turai.