Kocin Ghana ya ki daukar Abdul Majeed Waris

Abdul Majeed Waris na wasa ne a kungiyar Lorient ta babbar gasar Faransa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Rashin sanya Abdul Majeed Waris a tawagar ta Black Stars ya ba da mamaki

Kocin Ghana Avram Grant ya fitar da sunayen 'yan wasan kasar 23 da zai je da su gasar cin kofin Afirka a Gabon, ba tare da Abdul Majeed Waris da ke wasa a Faransa ba.

Rashin sa dan wasan na gaba mai shekara 25, wanda yake kungiyar Lorient a babbar gasar Faransa, Ligue 1, ya zo da mamaki.

Tawagar Ghanan ta Black Stars, ta kai wasan karshe na gasar ta cin kofin Afirka ta karshe da aka yi a 2015, amma Ivory Coast ta fitar da ita a fanareti.

Asamoah Gyan, na kungiyar Al Ahly ta Hadaddiyar Daular Larabawa, shi ne zai zama kyaftin din tawagar, yayin da Andre Ayew na West Ham zai zama mataimakinsa.

Kasar wadda ta dauki kofin sau hudu, tana rukuni na 4 (Group D) tare da Masar da Uganda da kuma Mali.