Kofin Afirka: Premier ta rasa 'yan wasa 23

Fafatawar karshe ta 2015 tsakanin Ivory Coast da Ghana

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ivory Coast ce ta dauki kofin na Afirka na 2015 bayan ta doke Ghana a bugun fanareti

Kasashe 16 da za su fafata a gasar cin kofin kasashen Afirka ta bana sun mika sunayen tawagar 'yan wasansu mai mutane 23 kowacce.

Daga cikin 'yan wasan da za su je gasar wadda za a fara ranar 14 ga watan Janairun nan, akwai 'yan wasan Premier 23.

Abin da zai sa wasu kungiyoyin gasar ta Ingila su yi kewar 'yan wasan.

Zakarun Premier Leicester da Sunderland da Stoke City su ne bulaguron 'yan wasan na Afirka zai dama fiye da saura.

Domin kowacce daga cikin kungiyoyin uku za ta rasa 'yan wasa uku.

Leicester za ta rasa Daniel Amartey na Ghana da Riyad Maharez da kuma Islam Slimani 'yan Algeria.

Sunderland wadda ke tsakiyar yakin tsira daga faduwa daga Premier za ta rasa 'yan wasan tsakiya Didier N'Dong na Gabon Da Wahbi Khazri na Tunisia da dan baya Lamine Kone na Ivory Coast.

A bangarenta Stoke za ta jure rashin Mame Biram Diouf na Senegal da Wilfried Bony na Ivory Coast da Ramadan Sobhi na Masar

West Ham da Crystal Palace da Watford da Hull City, su kuwa kowacce za ta yi kewar 'yan wasa biyu ne.

Yayin da Bournemouth da Everton da Liverpool da Manchester United da Southampton da Kuma Arsenal za su rasa 'yan wasa daya kowacce.

Kungiyoyi bakwai ne na Premier su kuwa ba abin da zai daga musu hankali kan tafiyar 'yan wasan na Afirka gasar a Gabon.

Kungiyoyin su ne; Chelsea da Tottenham da Manchester City da Middlesbrough da Swansea City da Burnley da kuma West Bromwich.

Wasu daga cikin kungiyoyin bakwai za su gode wa Najeriya, Zakarun Afirkan na 2013, da ba ta samu gurbi ba a gasar ta bana, saboda haka 'yan wasan kasar da ke kungiyoyinsu ba za su tafi ba.