Copa del Rey: Bilbao ta ci Barcelona 2-1

Williams ne ya ci kwallo ta biyu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Williams na murnar kwallon Athletic Bilbao ta biyu da ya ci

Athletic Bilbao ta doke Barcelona da ci 2-1 a gasar cin kofin Copa del Rey na Spaniya ranar Alhamis da dare.

Aduriz ne ya fara ci wa Athletic din kwallonta a minti 25, yayin da Inaki Williams ya kara ta biyu a minti na 28.

A minti na 52 kuma Messi ya rama wa Barca kwallo daya da bugun tazara na ban mamaki.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Messi ya rama kwallo daya da bugun tazara mai ban mamaki

Wasan shi ne na karon farko na kungiyoyin da suka kai zagayen 'yan 16 na gasar.

Da 'yan wasa tara masu masaukin bakin suka ci Barcelona.

A minti na 73 ne alkalin wasa ya ba wa Raul Garcia jan kati saboda ketar da ya yi wa Neymar.

Kuma minti 10 tsakani sai alkalin wasan ya kara ba wa Ituraspe shi ma dan Athletic Bilbaon jan kati, shi ma saboda ketar da ya yi wa Neymar din.

A ranar Laraba 11 ga watan nan na Janairu za su yi karo na biyu a Nou Camp.

Idan ba a manta ba, a ranar Laraba ne aka fafata a gasar tsakanin sauran kungiyoyi shida;

Alcorcón 0 - 0 Córdoba, da Real Socieda 3 - 1 Villarreal, da Real Madrid 3 - 0 Sevilla

A ranar Laraba 12 ga watan Janairu ne su kuma za su yi karo na biyu na wasannin a gidajen wadanda suka bakunce su a wannan karon na farko.