'Yar Najeriya ta zama gwarzuwar 'yar kwallon Afirka

Asalin hoton, AFP
Macen da ta fi fice a kwallo a shekarar 2017 Asisat Oshoala (a hagu) a lokacin da take karbar kyautar ta a bikin karrama jaruman kwallon kafan Afirka a Abuja.
'Yar wasan tawagar kwallon kafar matan ta Najeriya watau Super Falcons, Asisat Oshoala, ta lashe lambar yabon 'yar kwallon da ta fi fice a fagen tamaula a nahiyar Afirka.
A bikin karrama 'yan kwallon Afirkan da suka taka rawar gani a fagen wasan a nahiyar wanda aka gudanar a Abuja ranar Alhamis, an bai wa Asisat kyautar macen da ta fi fice a taka leda a Afirka.
'Yar kwallon, wadda ke buga wa Asernal Ladies wasa a gasar Premier ta mata a Ingila, ita ta lashe kyautar a bikin da aka gudanar a farkon shekarar 2015.