Madrid ta yi wasanni 39 ba a doke ta ba

La Liga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Real Madrid za ta ziyarci Sevilla a wasanta na La Liga na gaba

Real Madrid ta yi kan-kan-kan da Barcelona a tarihin buga wasanni 39 a jere ba tare da an doke ta ba.

Madrid ta yi wasa na 39 a ranar Asabar, inda ta doke Granada da ci 5-0 a gasar cin kofin La Ligar Spaniya kwantan karawar mako na 16 da suka yi a Santiago Bernebue.

Tun a minti na 32 da fara tamaula Real Madrid ta ci kwallaye hudu ta hannun Isco wanda ya zura biyu a raga da wadda Benzema da Ronaldo suka ci.

Cesemiro ne ya ci ta biyar bayan da James Rodriguez ya bugo kwallo a bugun tazara a minti na 58 ana murza-leda.

Rabon da a doke Madrid a wasa tun wanda Wolsburg ta samu nasara a kanta da ci 2-0 a wasan cin kofin Zakarun Turai a karawar daf da karshe a cikin watan Afirilun 2016.

Real Madrid tana mataki na daya a kan teburin La Liga da maki 40, sai Barcelona biye da ita da maki 34, yayin da Sevilla ke matsayi na uku da maki 33.

A kakar wasan 2015/16 Real Madrid ta kawo karshen yawan buga wasanni 39 ba tare da an doke Barcelona ba, inda ta zura mata kwallo 2-1 a ranar 2 ga watan Afirilun 2016 a gasar La Liga.