Watakila Ronaldo ya lashe kyautar gwarzon Fifa na 2016

Ballon d'Or
Bayanan hoto,

An zabo 'yan takara daga mai taka-leda a Atletico Madrid da Real Madrid da Barcelona

Cristiano Ronaldo ne ake tsammani zai lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya da hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, za ta karrama a Zurich a ranar Litinin.

A watan jiya ne Ronaldo ya lashe kyautar Ballon d'Or karo na hudu, bayan da ya doke Lionel Messi wanda suka yi takarar tare.

A shekarar 2016 ne hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta raba gari da mujallar Faransa mai gudanar da kyautar Ballon d'Or bayan hadin gwiwar shekara shida da suka yi.

Cikin wadanda suke takarar kyautar dan kwallon kafa na duniya na 2016 sun hada da Lionel Messi na Barcelona da kuma Antoine Griezmann na Atletico Madrid.

Haka kuma a ranar ta Litinin, Fifa za ta bayyana macen da ta fi yin kwazo a fagen tamaula da kuma mai horar da kwallon kafa namiji da mace da babu kamarsu a shekarar 2016.

An tsara cewar masu horar da tawagar mambobin Fifa da kyaftin-kyaftin da wasu 'yan jarida da kada kuri'a ta yanar gizo a karon farko da hukumar ta amince magoya baya za su yi ne zai tantance zakarun bana.