Ozil na son sanin makomar Wenger a Arsenal kafin ya saka hannu a yarjejeniya

Mesut Ozil

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wenger ne ya dauko Ozil daga Real Madrid a shekarar 2013

Dan kwallon Arsenal, Mesut Ozil, ya ce yana son ya san makomar kociyan kungiyar Arsene Wenger, kafin ya amince ya tsawaita zamansa a Emirates.

Dan wasan, wanda dan kwallon tawagar Jamus ne kuma saura watan 18 yarjejeniyar da ya kulla da Arsenal ta kare, yana tattaunawa da mahukuntan kungiyar domin ya ci gaba da murza-leda a Emirates.

Wenger, wanda yarjejeniyarsa da Gunners za ta kare a karshen kakar bana, shi ne ya dauko Ozil daga Real Madrid a shekarar 2013.

Ozil ya yi watsi da magandanun da ake yi cewar bai tsawaita yarjejeniyar ci gaba da wasa a Arsenal ba ne domin takaddama kan karin kudin da ya bukaci a yi masa.

Wenger mai shekara 67, ya fada a baya cewar zai yi iya kokarinsa ya ga manyan 'yan wasansa ciki har da Ozil da Alexis Sanchez sun ci gaba da zama a Arsenal.