Turmi biyu suka dambata babu kisa

Turmi biyu suka dambata babu kisa

Turmi biyu suka dambata a gidan damben Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja, Nigeria a ranar Lahadi da yamma.

Sauran wasannin da aka buga an tashi babu kisa tsakanin Na 'Yar Tasa daga Arewa da Shagon Isihun Shandam daga Kudu.

Karawa da aka yi tsakanin Shagon Indali daga Kudu da Na Bacirawa Karami daga Arewa tashi suka yi canjaras.

Sai wasan da Shagon Faya daga Kudu ya doke Autan Bello daga Arewa a turmi na biyu, da karawar da aka tashi babu kisa tsakanin Shagon Buzu daga Arewa da Shagon Babangida daga Kudu.

Mohammed Abdu ne ya hada rahoto.