Barcelona ta samu maki daya a Villareal

Spanish League
Image caption Barcelona ta hada maki 35 tana kuma mataki na uku a kan teburin La Liga

Villareal da Barcelona sun tashi wasa kunnen doki 1-1, a gasar cin kofin La Ligar Spaniya, wasan mako na 17 da suka fafata, a ranar Lahadi.

Villareal ce ta fara cin kwallo ta hannun Nicola Sansone, bayan da ya karbi tamaula a wajen abokin wasansa, Alexandre Pato wanda ke buga wa kungiyar wasa aro daga Chelsea.

Messi ya buga kwallo ta bugi turke, an kuma hana Barcelona fenariti a karawar, bayan da dan kwallon Villareal, Bruno ya taba tamaula da hannu a lokacin da Messi ya samu dama.

Daga baya ne Messi ya farke kwallo a bugun fenariti wanda hakan ya sa suka raba maki tsakaninta da Villareal.

Da wannan sakamakon Barcelona tana mataki na uku a kan teburin La Liga, kuma Real Madrid wadda ke matsayi na daya ta bai wa Barca tazarar maki biyar.

Labarai masu alaka