Fifa za ta yi kuri'a kan karin kasashe a gasar kofin duniya

Gasar cin kofin duniya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jamus ce ta lashe kofin duniya na 2014 da aka yi a Brazil wanda kasashe 32 suka fafata

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa za ta kada kuri'a domin fayyace dacewar kara yawan kasashen da ke shiga gasar cin kofin duniya zuwa 48 a ranar Talata.

Shugaban hukumar Fifa, Gianni Infantino ne ya bayar da shawarar yin hakan tun lokacin da yake takarar kujerar ta hukumar.

Infantino na fatan idan an amince da tsarin, wanda zai fara aiki a 2026, zai kunshi raba rukunni 16 dauke da kasashe uku a kowanne, inda biyu daga kowanne rukuni za su kai zagayen gaba.

Idan har shirin ya samu amincewa, zai zama karon farko da Fifa ta fadada yawan mambobinta da ke buga gasar cin kofin duniya, kuma rabon da ta yi hakan tun a 1998.

Infantino mai shekara 46, ya maye gurbin Sepp Blatter a matsayin shugaban Fifa cikin watan Fabrairun 2016.

Tun da farko Infantino ya bayar da shawarar a mayar da kasashen da suke buga gasar cin kofin duniya zuwa 40 daga 32 da ake da su a yanzu, daga baya ya ce ya kamata su zama 48.