Oscar ya je Shanghai SIPG da kafar dama

Chelsea

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Oscar ya koma Shanghai daga Chelsea a watan Janairu

Tsohon dan kwallon Chelsea Oscar ya ci kwallo a wasan farko da ya buga wa sabuwar kungiyar da ya koma Shanghai SIPG a kan kudi fam miliyan 60.

Dan kasar Brazil mai shekara 25, ya ci kwallo ne bayan ya canji dan wasa a fafatawar da suka doke Al-Batin ta Saudia da ci 2-1 a birnin Doha na Qatar.

Daga baya ne aka yi wa Oscar keta kuma alkalin wasa ya bayar da bugun tazara inda Lu Wenjum ya buga kuma ta fada raga.

Oscar ya ce "Na yi atisayen kwana biyu kacal a kungiyar, kuma daf ake da a fara gasar cin kofin kasar China, babu abin da muka sa a gaba sai samun nasarori a wasannin da za mu yi".

A cikin watan Maris ne za a fara gasar cin kofin China wadda ake kira da Chinese Super League.