Ya dangantakar Birtaniya da Amurka a gwamnatin Trump?

Boris Johnson zai yi ganawa ta farko da jami'an gwamnatin Trump mai jiran gado

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Sakataren harkokin wajen Birtaniya, Boris Johnson zai yi ganawa ta farko da jami'an gwamnatin Trump mai jiran gado

Sakataren harkokin wajen Birtaniya Boris Johnson zai gana da jiga-jigan 'yan majalisar dokokin Amurka a ranar Litinin a Washington.

Tun ranar Lahadi sakataren ya tattauna da wasu manyan makusantan Donald Trump, a ganawa ta farko ta keke-da-keke tsakanin wani ministan Birtaniya da jami'an sabuwar gwamnatin Amurkan mai jiran gado.

Jiga-jigan da zai gana da su 'yan jam'iyyar Republican sun hada da shugaban kwamitin kula da harkokin waje na majalisar, Bob Corker, da shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Mitch McConnell.

Bisa ga dukkan alamu sakataren harkokin wajen na Birtaniya zai tattauna da kusoshin ne kan inda manufar Amurka ta kasshen waje ta nufa a karkashin shugabancin Donald Trump.

Sakataren wajen na Birtaniya ya yi tattakin ne domin kokarin dawo da dangantakar Birtaniya da Amurka kan turba, sakamakon hannunka mai sanda da Mista Trump ya yi da farko ga tsohon jagoran jam'iyyar UKIP ta Birtaniya,Nigel Farage, na neman yin hakan.

A jiya ne dai Mr Johnson ya kasance ministan gwamnatin Birtaniya na farko da ya yi ganawa ta keke da keke da wasu daga cikin jiga-jigan gwamnatin Amurkan mai jiran gado.

A ganawar da suka yi a ginin Trump Towers da ke New York, Mista Johnson ya tattauna da sirikin Mista Trump Jared Kushner, da ke auren 'yar shugaban mai jiran gado, da Steve Bannon, babban mai tsara wa Trump din dabaru.

Jami'ai sun bayyana tattaunawar tasu a matsayin mai muhimmanci wadda ba wani boye-boye, a kan manufar Amurka ta haorkokin kasashen waje, musamman ma dai a kan Rasha.

A jiya Fira Ministan Birtaniya Theresa May ta ce ta yi tattaunawa biyu mai kyawun gaske da Mista Mr Trump, wanda shi ma har ya sanya sako a shafin Tweeter cewa yana fatan ganawa da ita a Washington a lokacin damuna.