Da sani na sa yara a tawagar Liverpool - Jurgen Klopp

Jurgen Klopp

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Jurgen Klopp ya kare matakin cika tawagar Liverpool da yara

Kociyan Liverpool, Jurgen Klopp, ya kare gabatar da 'yan tawagar kungiyar mafi karancin shekaru a tarihi a wasan da Liverpool ta tashi canjarans 0-0 da Plymouth.

Kungiyar wacce ta gabatar da 'yan wasan da yawancin su 'yan shekara 21 da kwanaki 296 ne sun kusan shan kwallaye biyu ta kafafun Sheyi Ojo da Daniel Sturridge, amma kungiyar kwallon kafan da ke murza leda a mataki na biyu ba ta sake musu ba.

Yanzu Liverpool na fuskantar zuwa Devon domin sake buga wasan zagaye na uku kuma suna da wasanni shida a watan Janairu.

Kocin wanda dan kasar Jamus ya ce: " Ba na ganin gabatar da jerin 'yan wasan kuskure ne."

Kungiyar Klopp na kuma fuskantar Southampton a wasanni biyu na dab-da-na -karshe da kuma wasannin Premier da Manchester United, da Swansea da kuma Chelsea a wannan watan.

Da aka tambaye shi game da balaguron tsakiyar makon da zai yi domin wasan da za'a buga ranar 17 ga watan Janairu, Klopp ya kara da cewar: "Aha. Ban san in za su iya buga irin wannan salon wasan tsare gida a gida haka ba. Muna sha'awar ganin yadda wasan zai kasance."

Dan wasan gaba, Ben Woodburn, mai shekara 17, shi ne dan kungiyar kwallon kafar mai shan kwallo mafi karancin shekaru bayan ya sha Leeds a gasar EFL a kakar bana. A bana aka bashi damar fara buga wasa ta farko.

Trent Alexander-Arnold, mai shekara 18, da Joe Gomez mai shekara 19 da Ovie Ejaria da kuma Ojo sun kasance cikin tawagar.

Lucas mai shekara 29 ne dan wasan Liverpool mafi shekaru a tawagar.

Asalin hoton, .

Bayanan hoto,

Duk da cewar taswirar rawar da Liverpool ta taka (a hagu) ya nuna rinjayen da suka samu a rike kwallo a wasan in aka kwatanta da taswirar Plymouth (a dama) - an tashi wasan babu shan kwallo

"Na dauki alhakin abin da ya faru in kana son ganin lamarin da matsala," inji Klopp.

"A kullum ina zaban tawaga ne domin samun nasara a wasa. Bamu yi tunanin shekaru ba. 'Yan wasa masu muhimmi ne a tawagar mu."

'Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne 'yan wasan da suka saba samun shiga wasa daga farkon lokaci irin su Daniel Sturridge da Adam Lallana da kuma Roberto Firmino suka samu shiga, amma masu karban bakuncin da suka samu rinjayen rike kwallo da kashi 80.3 cikin dari kafin a tafi hutun rabin lokaci sun cigaba da fruskantar takaici.

"Da rawar da muka taka ta fi haka, dari bisa dari," inji kocin Liverpool din da ake ce wa Reds. "Kafin hutun rabin lokaci mun gasa yin hakuri da wuri inda muka fara dago kwana a lokacin da bai dace ba kuma muka fara yin kuskure a ba da kwallo.

"Kwallon na hannun mu a ko wani lokaci. Wasan na gajiyarwa ne, not the most exciting game, ba mafi jan hankali ba ne."

Bayanan bidiyo,

FA Cup: Stunning goals from the third round

'Sannu da zuwa duniyar gaskiya'

Plymouth, who wadda ta kasance ta biyu kuma tana neman zuwa gasa ta biyu, ta hana Liverpool tabuka komai fiye da neman shan kwallaye hudu.

" Mai yiwuwa ne wasan ya zama wasan tsaren gida mafi kyau da Anfield ta taba gani," inji kocin Plymouth Derek Adams. "Mun ba su lokaci, amma ba mu basu wuri ba.

"Wannan lamari ne na aikin tawaga. Mun yi amfani da 'yan wasa 13, kuma dukkansu sun can-canci babban yabo."

Da aka tabaye shi me Liverpool za ta tsammani a zagaye na biyu a Home Park, ya ce: "Barka da zuwa duniyar gaskiya."